logo

HAUSA

Sin za ta hanzarta gina tsarin sanya ido kan muhallin halittu na zamani

2024-05-06 10:24:15 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar lura da muhalli da muhallin halittu ta kasar Sin Pei Xiaofei, ya ce Sin ta tsara wasu matakai da za a aiwatar, da nufin gaggauta gina tsarin sanya ido kan muhallin halittu irin na zamani.

Pei Xiaofei, ya kara da cewa, yanzu haka kasar ta riga ta kafa cikakken tsari mai game dukkanin sassa mafi girma a duniya a wannan fanni. Kaza lika, kasar za ta kyautata sassa masu rauni, a fannin lura, da kuma samar da mizanin karko a sashen, ta yadda za a kai ga samar da managarcin tsarin sanya ido kan muhallin halittu irin na zamani.  (Saminu Alhassan)