logo

HAUSA

Mataimakin firaminstan Sin ya bukaci a kara kaimi ga aikin ceto da agaji bayan ruftawar hanya

2024-05-03 15:48:48 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing ya jaddada cewa, ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan ceto da na agaji, biyo bayan ruftawar wani bangare na babbar hanyar mota da sanyin safiyar Laraba a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Zhang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da yake jagorantar aikin ba da agajin gaggawa na bala’in da ya afku a birnin Meizhou na lardin Guangdong.

Bayan umarnin babban sakataren kwamitin kolin JKS, Xi Jinping, da bukatar firaministan kasar Li Qiang, Zhang ya jagoranci jami’an da ke kula da sassan da abin ya shafa zuwa wurin da lamarin ya afku, domin jagorantar aikin ceto da ba da agaji.

Zhang ya ga yadda ake gudanar da ayyukan ceto a wurin, sa'an nan ya je asibitin jama'ar Meizhou don sanin yanayin da wadanda suka jikkata ke ciki, ya bukaci a gaggauta aikin ceto da kuma ba da magani.

Yayin da yake jagorantar wani taro kan aikin ceto da agajin bala'i a yammacin ranar Alhamis, Zhang ya bukaci a yi kokarin tabbatar da aikin ceto a kan lokaci da kuma rage nakasu ga wadanda suka jikkata. (Yahaya)