logo

HAUSA

Yawan ‘yan kasuwan ketare a Canton Fair karo na 135 ya zarce dubu 234

2024-05-03 16:29:07 CMG Hausa

Ya zuwa jiya 2 ga wata, baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin ko Canton Fair karo na 135, ya jawo hankulan ‘yan kasuwa 234671 daga kasashe da yankuna 215, wanda ya karu da kashi 25 cikin 100 idan aka kwatanta da na karo na 134. Kashi na uku na baje kolin Canton zai ci gaba har zuwa ranar 5 ga Mayu. Tare da taken “Kyakkyawar rayuwa”. Yana da rumfunan baje koli a cikin manyan sassa 5. Akwai kayan wasan yara da kayayyakin yara da mata masu juna biyu, da kayayyakin ado, da kayayyakin gida, da kayayyakin aiki, da na kiwon lafiya da nishadi. Akwai masu baje koli 11495, gami da masu baje kolin kayayyakin shige 262 daga kasashe da yankuna 29. (Yahaya)