logo

HAUSA

Binciken CGTN: Kashi 80 cikin 100 sun yaba da tasirin Sin a duniya

2024-05-02 15:26:35 CMG Hausa

A yayin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Faransa a ‘yan kwanaki masu zuwa, wani bincike da CGTN na rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ko CMG da jami’ar Remnin ta kasar Sin suka gudanar, ta cibiyar bincike kan harkokin sadarwa ta kasa da kasa ta New Era, ga masu ba da amsa na Faransa 1,513 ya nuna cewa, kashi 80.2 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa sun yi imanin cewa, kasar Sin kasa ce mai girma da tasiri, kuma kashi 70.3 cikin 100 daga cikinsu suna daukar kasar Sin a matsayin kasa mai nasara.

A binciken, kashi 71.7 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa sun yi imamin cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa na daga cikin muhimman alakar tsakanin kasashe biyu a duniya. Kashi 61.6 na wadanda suka ba da amsa na da kyakkyawan fata game da ci gaban da za a samu a nan gaba, kuma suna fatan bangarorin biyu za su kara karfafa hadin gwiwa kan tattalin arziki da cinikayya, kimiyya da fasaha, da kuma batutuwan siyasa na shiyya. (Yahaya)