logo

HAUSA

Xi ya amsa wasikar ma'aikatan kamfanin samar da karafa na Smederevo dake Serbia

2024-05-01 15:40:57 CMG Hausa

A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu ma'aikata 'yan kasar Serbia, na masana'antar samar da karafa ta Smederevo na kasar, wanda ke karkashin mallakar kamfanin HBIS na kasar Sin, suka aika masa, inda ya karfafa musu gwiwa, don su ci gaba da samar da gudunmowa a kokarin karfafa zumunta tsakanin kasashen Sin da Serbia.

A cewar shugaban na kasar Sin, yayin da ya kai ziyara kasar Serbia a shekarar 2016, ya ziyarci masana'antar samar da karafa ta Smederevo, inda ya yi hira da wasu ma'aikata, wadanda a lokacin suka nuna goyon bayansu ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Serbia, da bayyana kyakkyawan fata game da makomar masana'antarsu.

Shugaba Xi ya ce, bisa wasikar da wasu ma'aikatan masana'antar suka aika masa, ya san cewa, harkokin masana'antar sun samu ci gaba sosai, bisa kokarin aiki da jami'ai da ma'aikata na kasashen Sin da Serbia suke yi, wanda ya taimakawa kokarin raya tattalin arziki a birni na Smederevo. Har ila yau, shugaban ya ce yana farin ciki matuka, ganin yadda masana'antar samar da karafar ta fara samun riba cikin sauri, da kare guraben aikin yi na ma'aikata fiye da 5000, gami da tabbatar da jin dadin zaman rayuwar wasu magidanta fiye da 1000, bayan wani kamfanin Sin ya zuba jari a masana'antar.

Kafin haka, wasu ma'aikata 'yan kasar Serbia 30, na masana'antar samar da karafa ta Smederevo, sun rubuta wata wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, a madadin sauran ma'aikatan masana'antar, inda suka yi bayani kan yanayin da harkokin masana'antar ke ciki, da gudunmowar da ta samar a fannin kyautata rayuwar jama'ar wurin. Ban da haka, sun mika godiya ga shugaban na Sin, kan yadda ya kula da aikin zuba jari ga masana'antar samar da karafa ta Smederevo, gami da tabbatar da kammaluwar aikin. (Bello Wang)