logo

HAUSA

Yan sama jannatin Shenzhou-17 sun dawo doron duniya

2024-04-30 20:16:03 CMG Hausa

A yau Talata, ‘yan sama jannati 3 dake cikin kumbon Shenzhou-17 na kasar Sin da suka hada da Tang Hongbo da Tang Shengjie da kuma Jiang Xinlin, sun fito daga cikin sashen komawa na kumbon da ya sauka a tashar saukar kumbuna ta Dongfeng dake yankin Mongolia ta Gida mai cin gashin kansa a arewacin kasar Sin.

Hukumar kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce dukkan ‘yan sama jannatin 3 suna cikin koshin lafiya kuma sun kammala aikinsu cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)