logo

HAUSA

Kwamitin kolin JKS na 20 zai gudanar da zamansa na 3 a watan Yuli

2024-04-30 16:12:34 CMG Hausa

Kwamitin kolin JKS na 20 zai gudanar da zamansa na 3 a watan Yuli dake tafe a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. An amince da hakan ne yayin zaman zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS na Talatar nan. Kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ne ya jagoranci taron.

Bisa ajandar zaman kwamitin kolin JKS na 20 dake tafe, hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS za ta gabatar da rahoton aiki ga kwamitin tsakiya, kuma zaman zai nazarci batutuwa da suka jibanci kara zurfafa cikakkun sauye-sauye, da manufofin ingiza zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Har ila yau, zaman zaunannen kwamitin hukumar siyasar ya nazarci halin tattalin arziki da ake ciki da ayyukan raya fannin, ya kuma tattauna kan kundin bayani kan manufofi, da matakai, na ci gaba da ingiza cimma nasarar hadadden tsari mai inganci na bunkasa kogin Yangtze. (Saminu Alhassan)