logo

HAUSA

Wakilin shugaba Xi zai halarci taron shugabannin kungiyar OIC karo na 15

2024-04-30 20:07:52 CMG Hausa

Yayin taron manema labarai na yau da kullum na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin na yau Talata, kakakin ma’aikatar Lin Jian, ya bayyana cewa, wakilin musamman na shugaban Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, Zheng Jianbang, zai je kasar Gambia don halartar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa ta kasashe musulmi ko OIC karo na 15 da za a gudanar a Banjul, fadar mulkin Gambia, daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Mayu, bisa gayyatar da shugaban Gambia Adama Barrow ya yi masa.

Da yake tsokaci game da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dake cewa ya damu da yadda “Sin ta samar da kayayyaki fiye da yadda ake bukata”,Lin Jian ya bayyana cewa, wannan zargi da bangaren Amurka ke yayatawa, karya ce kawai don neman dakile ci gaba mai inganci na kasar Sin.

Game da yadda kamfanonin Sin da na ketare fiye da 1,500 da suka taru a bikin baje kolin motoci na kasa da kasa na Beijing, Lin Jian ya ce, alkaluman sun nuna kamfanonin samar da motoci suna da kwarin gwiwar samun karuwar kasuwa a kasar Sin.

Bugu da kari, don gane da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Turai, Lin Jian ya ce, ya kamata Sin da kasashen Turai su fahimci juna sosai, kana su hada hannu wajen tinkarar kalubalen da kasa da kasa ke fuskanta.

Har ila yau, kakakin ya yi tsokaci game da tattaunawar da aka yi kwanan nan tsakanin kungiyoyin Fatah da Hamas na Falasdinu a birnin Bejing don warware rikicinsu na cikin gida, inda ya bayyana cewa, lamarin ya nuna burin bangarorin biyu na warware rikicinsu ta hanyar tattaunawa. Ya kara da cewa, kungiyoyin sun yabawa kasar Sin bisa goyon bayan da take ba al’ummun Falasdinu wajen maido da halaltattun hakkokinsu. (Safiyah Ma)