logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bayyana matukar kaduwa bisa asarar rayuka sakamakon ambaliyar ruwa a Kenya

2024-04-30 10:40:37 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar kaduwa sakamakon asarar rayukan gwamman mutane a kasar Kenya, biyowa bayan ambaliyar ruwa da ta yi mummunan ta’adi a birnin Nairobi da sauran wasu sassan kasar.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, mista Guterres ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin kasar, da iyalan wadanda ambaliyar ruwan ta hallaka.

Ya ce tawagar MDD dake kasar na ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin Kenya, da abokan huldarta, tun fara saukar ruwan sama mai karfin gaske a farkon shekarar nan, da nufin samar da tallafin jin kai da ake bukata. (Saminu Alhassan)