logo

HAUSA

Sin na goyon bayan UNMISS da ta aiwatar da matakan da suka dace don tallafawa Sudan ta kudu kan babban zaben kasar da za ta yi

2024-04-30 15:36:13 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya bayyana a jiya Litinin cewa, Sin na goyon bayan tawagar musamman ta MDD dake aiki a Sudan ta kudu wato UNMISS, da ta dauki matakan da suka dace na tallafawa kasar wajen cimma nasarar babban zabe bisa halin da take ciki da bukatunta.

Dai Bing ya kara da cewa, ya kamata a mutunta ikon mulki, da alfarmar jagorancin kasar yayin gudanar da wannan aiki. Tare kuma da jin ra’ayin Sudan ta kudu, don kaucewa manufofi da sauran sassa za su dora mata da suka sabawa halin da ake ciki.

Dai Bing ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa a yayin da ake kada kuri’a kan daftarin shirin tsawaita wa’adin aikin UNMISS, inda ya kara da cewa, kasar Sin na marawa tawagar baya, bisa sauke nauyin dake wuyanta, amma daftarin shirin da aka zartas ba da dadewa ba, ya yiwa gwamnatin wucin gadin kasar matsin lamba da yawa a bangarori daban-daban, kuma ayyukan da aka dorawa UNMISS sun sabawa da halin da ake ciki.

Har ila yau, daftarin ya yi zargi da kakkausar murya, kan gwamnatin Sudan ta kudu, game da batun babban zaben kasar da sauransu, har ma ya tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, matakin da ya wuce misali, kuma hakan ya sa Sin kin jefa kuri’arta. (Amina Xu)