logo

HAUSA

Tafiye tafiye ta jirgin kasa a Sin yayin hutun bikin May Day za su kai miliyan 144

2024-04-29 20:16:41 CMG Hausa

Kamfanin zirga zirgar jiragen kasa na kasar Sin, ya ce mai yiwuwa ne adadin tafiye tafiye da za a yi ta jiragen kasa, yayin hutun bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya zai kai miliyan 144.

Kamfanin ya ce cikin wa’adin hutun bikin na “May Day” na kwanaki 8, ana sa ran ranar Laraba ta zamo mafi yawan zirga zirgar jiragen kasa, inda ake hasashen samun tafiye tafiye ta jiragen kasan har kimamin miliyan 21. (Saminu Alhassan)