logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai ziyarci kasashen Faransa da Serbiya gami da Hungary

2024-04-29 16:14:42 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasashen Faransa da Serbiya da Hungary, daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Mayu.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ce ta sanar da hakan a yau Litinin, inda ta ce shugaba Xi Jinping zai kai ziyarar ce bisa gayyatarsa da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, da shugaban kasar Serbiya, Aleksandar Vučić, da shugaban kasar Hungary Sulyok Tamás gami da firaministan kasar Orbán Viktor, suka yi. (Murtala Zhang)