logo

HAUSA

CMG ya gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyoyin yayata tasharsa ta 8K UHD

2024-04-28 16:41:20 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya gudanar da bikin sanya hannu kan takardun yarjejeniyoyin yayata tasharsa ta talabijin, mai kunshe da fasahohin zamani masu karkon hotuna da sautu ko 8K UHD, a babbar cibiyar kasa da kasa ta watsa labarai ta Shanghai, wadda ke birnin Shanghai na gabashin kasar Sin.

An sanya hannu kan takardun yarjejeniyoyin ne don samar da ababen bukata ga tashar, da suka hada da shirye shirye, da dandaloli da fasahohi. Kaza lika, sassan da suka sanya hannu kan takardun yarjejeniyoyin sun hada da manyan jami’ai daga kamfanin kasa da kasa na raya al’adu na Shanghai, da kamfanin watsa shirye shiryen talabijin na dijital na kasar Sin, da kamfanin hidimar ajiyar bayanai na Alibaba reshen birnin Shanghai.

Tun a watan Janairun shekarar 2022 ne aka kaddamar da tashar talabijin ta 8K UHD, wadda ake fatan za ta yi amfani da gajiyar ta wajen yayata ci gaban sashen watsa shirye shirye, na masana’antun fasahohin 8K, tare da gabatarwa jama’a da ingantattun hotuna, da muryoyi mafiya inganci.    (Saminu Alhassan)