logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Shirya Harba Na’urar Binciken Wata Ta Chang’e-6

2024-04-27 16:00:05 CMG Hausa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin CNSA ta bayyana cewa, farkon watan Mayu ne lokacin da ya dace a harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6.

A yau Asabar ne aka yi jigilar na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 da kuma rokar dakon kaya kirar Long March-5 Y8 zuwa wurin harba kumbuna a cibiyar harba kumbuna ta Wenchang da ke lardin Hainan a kudancin kasar Sin, a cewar CNSA. 

Bayan da na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 da kuma rokar dakon kaya kirar Long March-5 Y8 suka isa wurin da ake harba kumbuna a watan Janairu da na Maris bi da bi, aikin harhadawa, da gwaji da sauran shirye-shirye an kammala su cikin nasara.

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 za ta tattara samfurori daga jefen duniyar wata mai nisa, wanda zai kasance aikin bincike irinsa na farko a tarihin dan Adam. (Yahaya)