logo

HAUSA

Sauyin yanayi na iya haddasa karuwar kwayoyin cuta masu bijirewa magani

2024-02-19 20:14:20 CMG Hausa

 

Hukumar tsara shiri kan muhalli ta MDD ta fitar da wani rahoto a kwanan baya, inda a ciki ta bayyana cewa, watakila sauyin yanayi da sauran dalilai masu nasaba da muhalli, su kara karfin wasu kwayoyin cuta na bijirewa magani, hakan na iya sa yawan kwayoyin cuta masu bijirewa magani zai karu sosai.

Rahoton ya ruwaito cewa, a shekarar 2019, mutane kimanin miliyan 5 ne a duniya suka riga mu gidan gaskiya saboda yadda kananan kwayoyin halittu da ido ba ya iya gani, bijirewa magani. Idan ba a dakile karfinsu na bijirewa magani ba, to, ana hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2050 yawan mutanen da za su mutu sakamakon hakan, zai karu zuwa miliyan 10 a ko wace shekara.

Dangane da illolin da kwayoyin cuta masu kin jin magani suke haifarwa, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, a ko da yaushe kwayoyin cuta na bijirewa magani, amma yadda jama'a ke shan maganin yaki da kwayoyin cuta barkatai, yana kara ta'azzara matsalar. Kwayoyin cuta masu kin jin magani sun fi yaduwa, inda suke bai wa takwarorinsu kwayoyin halitta kin jin magani.

A baya, ana ganin cewa, yadda ake shan maganin yaki da kwayoyin cuta barkatai, ya sa kwayoyin cuta bijirewa magani, amma akwai karin shaidu da ke nuna cewa, muhalli shi ma wani dalili ne mai muhimmanci. Alal misali, karuwar yanayin zafi tana kara saurin yadda kwayoyin cuta suke girma, ta yadda hakan zai kara saurin yadda kananan halittu suke gadar kwayoyin halittar dake kin jin magani.

Har ila yau, sauyin yanayi kan haddasa karin ambaliyar ruwa mai muni, lamarin da watakila zai haddasa cunkuson mutane a matsugunai, tabarbarewar muhallin matsugunan, da tsanantar gurbatar muhalli. Ta haka karuwar najasa da karafa masu nauyi da sauransu a ruwa, za ta taimakawa irin wadannan kananan halittu kara kin jin magani.

Kamar yadda madam Inger Andersen, darektar zartaswa ta hukumar tsari shiri kan muhalli na MDD ta fada, wasu dalilai masu nasaba da tabarbarewar muhalli suna tsananta matsalar ingantuwar karfin kwayoyin cuta na kin jin magani, lamarin da zai lalata tsarin kiwon lafiya da samar da abinci. (Tasallah Yuan)