logo

HAUSA

Karfafa dangantakar soja tsakanin Sin da Nijar a tsakiyar tattaunawa tsakanin minista Salifou Mody da jakada Jiang Feng

2024-04-24 10:19:26 CMG Hausa

A ranar jiya Talata 23 ga watan Afrilun shekarar 2024, ministan tsaron kasar Nijar janar Salifou Mody ya gana a birnin Yamai tare da jakadan kasar Sin da ke Nijar mista Jiang Feng, inda jami’an biyu suka maida hankali wajen ingiza da karfafa dangantakar soja a tsakanin kasashen biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A yayin wannan ganawa, ministan tsaron kasar Nijar Salifou Mody da jakadan kasar Sin da ke Nijar Jiang Feng sun tabo kyaukyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, musammun ma a fannin tsaro. Inda suka jaddada niyyarsu ta karfafa da zurfafa wannan dangantaka domin amsa kalubalen tsaro.

Haka zalika, wannan ganawa tsakanin manyan jami’an biyu ta kammala tare da sakamako mai armashi, bisa niyyar kasashen biyu wajen karfafa dangantakarsu a fannin tsaro. Tare da yin imanin cewa wannan dangantaka za ta taimakawa ga zaman lafiya da dorewar kwanciyar hankali a yankin Sahel.

Kasashe Nijar da Sin suna raya huldar dangantaka mai karfi ganin cewa dangantakar soja na taka muhimmiyar rawa wajen karfafa wannan hulda. Musanya tsakanin minista Salifou Mody da jakada Jiang Feng na shaida niyyar kasashen biyu na ci gaba da zurfafa wannan dangantaka domin fuskantar kalubalen tsaro da tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a yankin Sahel.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.