logo

HAUSA

Masu aikin sa-kai na kaiwa tsoffi abinci ba tare da sun karbi kudin hidima ba

2024-05-01 00:02:52 CMG Hausa

A garin Xiepu dake yankin Zhenhai na birnin Ningbo dake lardin Zhejiang na kasar Sin, akwai gungun wasu “masu aikewa da sakwanni” na musamman, wadanda ke kaiwa tsofaffi abinci ba tare da sun karbi kudin hidima ba, musamman tsofaffin dake rayuwa su kadai, da tsoffi wadanda ke da bukata ta musamman a wurin.

Masu aikewa da sakwannin, tsoffi ne masu aikin sa-kai dake wurin, ciki har da wani mai shekaru 64 a duniya.