logo

HAUSA

Turai: Mutane dubu 195 sun rasa rayukansu sakamakon yanayi mai tsanani a shekaru 40 da suka wuce

2024-02-12 14:56:26 CMG Hausa

 

Hukumar kula da muhalli ta Turai EEA ta gabatar da rahoto a kwanan baya cewa, daga shekarar 1980 zuwa 2021, mutane kusan dubu 195 ne suka rasa rayukansu a kasashen Turai, sakamakon yanayi mai tsanani, tare da yin asarar kudi har Euro biliyan dari 5 da miliyan 60.

A cikin rahotonta, hukumar EEA ta yi nuni da cewa, a cikin wadannan shekaru 42 da suka wuce, mutane kusan dubu 195 sun rasa rayukansu ne sakamakon ambaliyar ruwa, mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama, tsananin zafi, tsananin sanyi, gobarar daji da zabtarewar kasa. A cikin wadannan bala’u, yawan wadanda suka mutu sakamakon tsananin zafi ya kai kashi 81 cikin kashi 100. Yayin da tsananin yanayi ya haddasa asarar kudi har Euro fiye da biliyan dari 5 da 60, ciki har da wasu kashi 56 cikin kashi 100 biyo bayan ambaliyar ruwa.

A shekarar 2022, kasashen Turai sun dauki lokaci mai tsawo suna fama da tsananin zafi, inda mutane da dama suka mutu. Amma hukumar EEA ba ta bayyana adadin na shekarar 2022 a cikin rahotonta ba. Bayanan hukumar EEA sun nuna cewa, yawan mutanen da suka mutu a watan Yulin shekarar 2022 ya karu da kashi 16 cikin kashi 100, wato dubu 53, gwargwadon matsakaicin yawan mutuwar mutane daga shekarar 2016 zuwa ta 2019. Dalilin kai tsaye da ya haddasa mutuwar wadannan mutane shi ne tsananin zafi. A kasar Sifaniya kuma mutane dubu 4 da dari 6 sun rasa rayukansu ne sakamakon tsananin zafi daga watan Yuli zuwa na Agusta na shekarar 2022, wadanda mutuwarsu ta wuce yadda aka yi hasashe.

Hukumar EEA ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan ba da kariya, musamman ma ga tsofaffi. A cewar hukumar, ko da yake yawancin kasashe sun yi la’akari da sauyin yanayi wajen tsara manufofi da matakan kiwon lafiyar al’umma, sun kuma kara fahimtar illolin da tsananin zafi ke haifarwa ga jijiyoyin dake kai jini cikin zuciya da kuma tsarin sassan jiki dake taimakawa numfashi, amma wasu da yawansu bai kai rabi ba sun yi la’akari da illolin kai tsaye da tsananin zafi ke kawowa, kamar rashin isasshen ruwa a jiki da kuma suma sakamakon tsananin zafi.

Hukumar EEA ta ba da shawarar cewa, wajibi ne kasashen Turai su gaggauta fito da tsari don kaucewa kara asarar rayuka da dukiya, a maimakon daukar matakai biyo bayan gamuwa da matsalar tsananin zafi da sauran yanayi mai tsanani. (Tasallah Yuan)