logo

HAUSA

An kawo shawarar samar da cibiyar dakile ayyukan ta`addanci a kasashen dake Nahiyar Afrika

2024-04-23 09:47:44 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kiran da a kafa  wata cibiyar yaki da ta`addanci da musayar bayanan sirri ta bai daya a kasashen dake Nahiyar Afrika.

Ya bukaci hakan ne ranar Litinin 22 ga wata a birnin Abuja a wajen babban taron shugabannin kasashen Afrika a kan yaki da ta`addanci a  Afrika, ya ce wajibi ne kasashen Afrika sun fara yakar talauci da yunwa kafin zuwa mataki na gaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinunu ya ce baya ga yaki da ta`addanci, ayyukan cibiyar za su hada da tabbatar da hadin kai a tsakanin kasashe da kuma cusa kuzari a zukatan al`umomin kasashen wajen shiga ayyukan dogaro da kai. 

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce lokaci ya wuce da za a rinka yakar ayyukan ta`addanci ta hanyar nuna karfi, inda ya ce matakin farko shi ne mahukunta su fara bincikar tushen bala’o’i kamar talauci da rashin daidaito a tsakanin al`umma da kuma adalci ga kowa.

Har ila yau shugaba ya ce ya zama wajibi kasashen dake nahiyar Afrika su kara karfi ga tsoffin tsare-tsarensu na yaki da ta`addanci kamar hadakar sashen kwararru kan bayanan sirri dake Abuja, da cibiyar nazarin bincike kan ayyukan ta`addanci a Afrika dake Aljeriya da kuma kwamitin tsaro da ayyukan sirri na Afrika dake Addis Ababa.

“Najeriya za ta cigaba da kokarin yaki da ayyukan ta`addanci da ayyukan masu tada kayar baya, muna kara inganta shirin mu na yaki da ayyukan ta`addanci ta hanyar samar da dokar hukunta masu aikata ayyukan ta`addanci da kuma dakile ci gaba da ayyukan ta`addanci a Najeriya”

Amma duk da haka shugaba Tinubu ya ce samar da cibiya ta bai daya a kan yaki da ayyukan ta`addanci a Afrika shi ne abu mafi dacewa, maimakon aiki  a ware, saboda sau tari masu aikata irin wannan munmunan aiki suna da rassa ne a kasashen daban daban dake Nahiyar.(Garba Abdullahi Bagwai)