logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin gina wasu gadoji guda biyu akan kudi sama da naira biliyan 14

2024-04-22 10:46:48 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin ginin tagwayen gadojin sama da na kasa a unguwar Tal`udu dake ciki birnin Kano, wanda aka kiyasta za a kashe naira sama da biliyan 14.

A lokacin da yake kaddamar da aikin a karshen makon jiya, gwamnan jihar ta Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce aikin gadar daya ne daga cikin jerin ayyukan gadoji da za a gudanar da aikin su cikin wannan shekarar, wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin wato TEC zai gudanar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce jihar Kano, jiha ce dake samun karuwar yawan jama`a a kai a kai, wanda kididdiga ya nuna akwai mutane sama da miliyan 25 da suke zaune a jihar.

Haka kuma hada-hadar kasuwanci shi ma sai cigaba yake yi da bunkasuwa a jihar, inda a kowacce rana ana samun dubban `yan kasuwa da suke shigowa cikin birnin kano daga sassan Najeriya da ma kasashe makwafta domin yin sayayya.

Wannan ne kamar yadda gwamna ya fada, gwammati ta ga dacewar fadada hanyoyin mota domin saukakawa al`umma da `yan kasuwa wajen zirga zirga.

Ya ce baya ga gina gadoji, haka kuma gwamnati na fadada sauran ayyukan raya kasa da walwalar al`ummar kamar gina asibitoci, makarantu da inganta sha`anin muhalli .

 “In Allah ya yarda za mu zuba ido mu tabbatar da cewa wadannan `yan kwangila sun yi aiki a lokacin da ya kamata su yi kuma sun gama a lokacin da ya kamata su gama, da ma dai su ba baki ba ne a jihar kano, sun yi ayyuka ingantttu a jihar Kano, wannan kamfani na TEC  shi ne ya yi maku gada ta sama ta kofar Nasarawa, shi ne ya yi maku gada ta sama ta hanyar Murtala Muhammed wadda duk a Najeriya babu gada mai tsawonta, sabo da haka muna da yakini in Allah ya yarda wannan kamfani zai yi wa al`ummar jihar Kano aiki ingantacce kamar yadda ya kamata”

Ana sa ran kammala aikin cikin kasa da watanni 18 masu zuwa.(Garba Abdullahi Bagwai)