logo

HAUSA

An gudanar da bikin ranar harshen Sinanci ta duniya a birnin Abuja dake tarayyar Najeriya

2024-04-21 16:40:28 CMG Hausa

Kasar Sin tana fatan za a kara fadada sha’anin zuba jari a bangaren kare yaruka ta hanyar karfafa ilimin harsuna biyu domin share fagen cikakken hadin kai a tsakanin al’ummomi mabanbanta.

Daraktan cibiyar raya al’adun kasar Sin a Najeriya Mr. Li Xuda ne ya bukaci hakan yayin bikin ranar harshen Sinanci na duniya da cibiyar ta shirya ranar 20 ga wata a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Mr. Li Xuda ya ce cibiyar al’adun kasar Sin dake Najeriya ta shafe shekaru 10 tana koyar da Sinanci tun bayan kafa ta a 2013, kuma ’yan Najeriya da dama sun ci gajiyar ta hanyar koyon Sinanci.

“Harshen mu abun alfaharin mu, ku zo mu hadu mu gudanar da bikin ranar harshen Sinanci, mu yi aiki tare domin tabbatar da burikan kasar China da na Najeriya, wadanda dukkansu sun shafi zaman lafiya da kaunar juna da cigaba da kuma hadin kai.”

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, babban sakatare a ma’aikatar raya al’adu ta tarayyar Najeriya Mr. James Sule kira ya yi ga masu ruwa da tsaki a Najeriya da su yi koyi da kasar China ta fuskar kokarin yada al’adun kasar a duniya baki daya.

“Ina tabbatar da cewa, ma’aikatar raya al’adu za ta goyi bayan duk wani shiri da zai karfafa gwiwar ‘yan Najeriya wajen koyon yaren Sinanci.”

Yanzu haka kai kasar China ta samar da makarantun koyon harshen Sinanci da kuma cibiyoyin raya al’adu da dama a sassa daban daban na Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)