logo

HAUSA

Shugaban rundunar sojojin sama na kasar Cadi ya umurni Amurka da ta dakatar da ayyukanta na sojoji a sansanin sojan Adji Kossei

2024-04-20 17:11:28 CMG Hausa

A ranar jiya, Juma’a 19 ga watan Afrilun shekarar 2024, gwamnatin kasar Cadi ta bukaci kasar Amurka da ta dakatar da ayyukan soja da ke yi a cikin kasar, bayan da jami’an sojojin Amurka suka kasa ba da cikakkun takardun shaidar kasancewarta a wannan kasa.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan wasika da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu kofinta, tun a ranar 4 ga watan Afrilu aka aika ta da ministan rundunar sojojin Cadi, manjo janar na sojojin sama Idriss Amine Ahmed, ya bukaci kasar Amurka da ta dakatar da ayyukan soja a sansanin sojojin sama na Adji Kossei, da ke kusa da birnin N’Djamena, bayan da kasar Amurka din ta kasa ba da cikakkun shaidu na kasancewarsu a wannan sansani.

Saidai kakakin gwamnatin Amurka ya bayyana cewa muna nan muna tattaunawa tare da shugabannin Cadi kan makomar dangantakar soja da ta tsaro tare da kasar Cadi, alhali kuma kasar na mai da hankali kan shirye shiryen zabukan shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa, muna tsinkayen yin shawarwari kan batutuwan dangantakarmu ta fuskar tsaro bayan wadannan zabuka, in ji kakakin.

Kasar Amurka na da kusan sojoji 100 a kasar Cadi, da ke kula da ayyukan tsare tsare game da yankin, in ji wani jami’in kasar Amurka. (Mamane Ada)