logo

HAUSA

Sri Lanka na mutuntawa da amincewa da kasar Sin, in ji firaministan kasar

2024-04-20 21:31:44 CMG Hausa

Firaministan kasar Sri Lanka Dinesh Gunawardana, ya yi zantawa ta musamman da ‘yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, yayin ziyarar da ya yi a kasar Sin a kwanakin baya, inda ya musanta ikirarin kasashen yammacin duniya, na cewa wai akwai wani "tarkon bashi" da kasar Sin ta kafa. Ya ce har kullum, Sri Lanka na mutuntawa, da kuma amincewa da kasar Sin.

Mista Gunawadana ya ce, "Har kullum Sri Lanka na mutuntawa da amincewa da kasar Sin, kuma tana fatan samun ci gaba tare da kasar Sin. Ya ce taimakon da Sin ke bayarwa na kara azama ga bunkasuwar kasar Sri Lanka. Baya ga haka, lokacin da Sri Lanka ke fama da matsaloli da wahalhalu, Sin ta kan tashi tsaye don taimaka mata. Kaza lika a yayin da Sri Lanka ke fuskantar barazana game da cikakken yankin kasa, ko kuma gab da wargajewar kasar, Sin ta nuna cikakken goyon-baya ga Sri Lanka wajen yaki da ta’addanci, da kare mulkin kai da cikakken yankin kasa. "

Firaminista Gunawardana ya kara da cewa, "Ina matukar godiya ga kasar Sin". (Mai fassara: Bilkisu Xin)