logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi musayar sakon taya murna da shugaban rikon kwarya na Gabon game da cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin sassan biyu

2024-04-20 16:32:54 CMG Hausa

Yau Asabar, 20 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musayar sakon taya murna da shugaban rikon kwarya na kasar Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema, game da cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakon, shugaba Xi ya nuna cewa, a cikin rabin karnin da ya gabata, duk da yadda yanayin da ake ciki a duniya ke ci gaba da canjawa, kasashen Sin da Gabon sun ci gaba da daukar juna daidai, kana suna goyon bayan juna, yayin da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ke kara ingantuwa, wanda hakan ya haifar da fa'ida ta gaske ga jama'ar kasashen biyu.

Xi Jinping ya kara da cewa, yana mayar da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Gabon, kuma yana son yin aiki tare da shugaba Nguema, don daukar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a matsayin wani sabon mafari, na ci gaba da sada zumuncin gargajiya tsakanin kasashen biyu, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa, da wadatar da abubuwan da suka shafi dangantakar abokantaka, ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kuma hada gwiwa don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da kasashen Afirka.

A nasa bangaren, shugaba Nguema ya bayyana cewa, kasarsa na tsayawa kan bin manufar Sin daya tak, kuma ta yi imanin cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi ba. Ya ce kasar Gabon tana son yin aiki tare da kasar Sin, wajen ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu gaba, tare da amfanar da jama'ar kasashen biyu.

A wannan rana kuma, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Gabon Ali Akbar Onanga Y’obeghe, sun aike da sako ga juna, don taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)