logo

HAUSA

Babban jami’in JKS zai halarci taro kan tsaro a Rasha

2024-04-20 18:12:52 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar kula da harkokin siyasa da shari’a na kwamitin kolin JKS Chen Wenqing, zai ziyarci kasar Rasha, domin halartar taro karo na 12, na manyan wakilan dake tattauna batutuwan tsaro, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da aka yi masa.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, mista Chen zai gudanar da ziyarar ne tun daga yau Asabar 20 ga wata zuwa 28 ga watan nan na Afirilu. (Saminu Alhassan)