Me ya sa ake ganin kasuwar Sin tana janyo hankulan kasa da kasa?
2024-04-19 11:19:34 CMG Hausa
Yayin bikin baje kolin kayyayakin amfani na kasa da kasa na Sin, wato CICPE karo na 4 da aka kammala a jiya Alhamis, mamallakin kamfanin salula na XOR na kasar Burtaniya Hutch Hutchison ya bayyana cewa, cikin ’yan shekarun nan, kamfaninsa ya dukufa kan aikin shiga cikin kasuwar kasar Sin, shi ya sa a bana, ya cimma nasarar halartar bikin na CICPE.
A bana, fitattun kamfanoni sama da dubu 4 daga kasashe da yankuna 71 sun halarci bikin, kuma adadin kamfanonin kasashen waje da suka halarci bikin ya zarce na bara. A yayin bikin, an nuna sabbin kayayyaki guda 1462, yayin da tamburan kamfanonin kasar Sin, da na kasashen waje guda 84 suka fito a karo na farko. Kana, a karon farko, kasashen Burtaniya, da Mongoliya, da Malasiya, da kuma wasu kasashen duniya sun turo tawagoginsu zuwa bikin.
Kasuwanni su ne albarkatu da jama’a suka fi bukata. A ganin kamfanonin kasashen duniya, manyan kasuwannin kasar Sin suna iya samar da kudaden shiga da yawa gare su. Kuma a halin yanzu, kasar Sin tana dukufa wajen farfadowa, da kuma habaka kasuwannin saye da sayarwa a cikin gida.
Bugu da kari, a ganin kamfanonin kasashen duniya, kasuwannin kasar Sin za su samar musu karfin yin kirkire-kirkire. A yayin biki na wannan karo, an gabatar da sabbin kayayyaki da dama wadanda aka kera su bisa fasahohin kasar Sin. Ban da haka kuma, yanayin kasuwanci mai bude kofa ga waje, kuma mai inganci a kasar Sin, ya samar da damammaki masu kyau ga kamfanonin ketare.
Abin da ya kamata a ambata shi ne, bayan fara aiwatar da manufar “Wasu dalilan da za su sa al’ummar kasashe 59 su shiga lardin Hainan na kasar Sin ba tare da gabatar da biza ba”, tun daga watan Fabarairun bana, baki daga kasashen duniya mai tarin yawa sun halarci bikin na wannan karo ba tare da gabatar da biza ba, lamarin da ya nuna burin kasar Sin na kara bude kofa ga waje, ta yadda kamfanonin kasashen duniya za su sami karin damammaki, da bunkasuwa a cikin kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)