logo

HAUSA

Sin ta nuna rashin gamsuwa da barazanar da Amurka ta yi na kara haraji kan karafa da gorar ruwa dake shiga kasar daga kasar Sin

2024-04-19 20:19:32 CMG Hausa

Dangane da barazanar da Amurka ta yi na kara haraji kan karafa da gorar ruwa da ke shiga kasar daga kasar Sin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a, a gun taron manema labaru da aka saba yi cewa, matakin na Amurka ya illata dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da Sin, kuma ya sabawa ra’ayin bai daya da aka cimma a yayin tattaunawar shugabannin kasashen biyu da aka yi a birnin San Francisco.

Kakakin ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka da ta shude ta kara haraji kan karafa da gorar ruwa na wasu mambobin kungiyar cinikayya ta WTO bisa hujjar wai "tsaron kasa", wanda kungiyar ta riga ta yanke hukunci cewa, matakin ya karya ka'idojinta. Amurka ba gaza gyara kuskurenta kadai ta yi ba, har ma tana barazanar kara haraji tare da sanar da kaddamar da wani sabon bincike bisa ayar doka ta 301, wanda ke kara yin kuskure. Ya ce kasar Sin za ta sa ido sosai kan yadda binciken ke gudana, tare da daukar dukkan matakan da suka dace don kare hakki da muradunta.

A yayin da yake ba da amsa kan kara wa batun “wuce gona da iri wajen samar da hajoji a Sin” gishiri da Amurka ta yi a baya-bayan nan, kakakin ya bayyana cewa, abin da ake kira "ra’ayin wuce gona da iri wajen samar da hajoji a kasar Sin" da Amurka ta gabatar, tamkar wani batu ne da ya danganci tattalin arziki, amma hakika mugun nufin kasar ne na murkushe ci gaban masana'antun kasar Sin, da nufin neman wani matsayi mafi dacewa na yin takara da samun fifiko a kasuwa, wanda ya kasance wani mataki na cin zali da matsawa kasar Sin ta fuskar tattalin arziki a bayyane. (Mai fassara: Bilkisu Xin)