logo

HAUSA

UNECA: Nahiyar Afirka ba ta kai ga cimma muradun SDGs ba

2024-04-19 11:36:24 CMG Hausa

Babban sakataren hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta MDD ko UNECA mista Claver Gatete, ya ce kasashen nahiyar Afirka sun gaza cimma muradun ci gaba mai dorewa na MDD ko SDGs, duk da cewa nahiyar ta yi namijin kokarin jure tarin kalubale da ba ita ta kirkire su ba.

Wata sanarwa da UNECA ta fitar, ta hakaito mista Gatete na cewa, fatara da yunwa, sun karu a sassan nahiyar cikin shekaru 5 da suka shude, a gabar da kasashen Afirkan ke fama da karuwar bashi, da matsalolin kudi da na sauyin yanayi. 

Jami’in ya kara da cewa, duk da hasashen ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka da aka yi na karuwar kaso 3.5 bisa dari a bana, sama da kaso 2.8 bisa dari da aka samu a shekarar 2023, wannan ci gaba bai kai matsayin da zai baiwa nahiyar damar cimma muradunta na nan zuwa shekarar 2063 ba.   (Saminu Alhassan)