logo

HAUSA

Tattalin arzikin kasar ya fara da kafar dama a farkon bana

2024-04-19 21:37:43 CMG Hausa

Tattalin arzikin kasar Sin ya fara da kafar dama a bana, inda harkokin kasuwanci su ka ci gaba da kasancewa a wani yanayi mai daidaito da inganci a rubu’in farko na bana, mataimakin ministan ma’aikatar Guo Tingting, ya ce lamarin ya ci gaba da bayar da kyakkyawar gudunmuwa ga farfadowar da tattalin arzikin kasar ke yi.

Cikin rubu’in na farko, kasar ta samu karuwar kaso 5.3 a GDPnta, wanda ya samu daga karuwar sayyayya da ya mamaye kaso 73.7 na ci gaban, haka kuma ya ingiza karuwar GDPn da maki kaso 3.9.

Harkokin cinikayya ma sun samu mafari mai kyau, inda yawan kayayyakin da aka yi cinikayyarsu ya kai matsayin koli zuwa yuan triliyan 10.2, kwatankwacin dala triliyan 1.43, karon farko cikin rubu’i daya, inda ya samu karuwar kaso 5, adadi mafi yawa da aka samu cikin rubu’i 6 da suka gabata. Wannan ci gaba ya samu ne daga karuwar fiton kayayyaki, wanda ya bayar da kaso 14.5 ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

A fannin jarin waje kuwa, an samu kafuwar sabbin kamfanoni masu jarin waje sama da 12,000 a rubu’in na farko na bana, karuwar kaso 20.7. Fannonin da aka zuba jarin ma sun fadada, musamman a fannin samar da kayayyakin bangaren ingantattun fasahohi, wanda ya ja jarin kaso 12.5 na jimlar jarin waje, karuwar maki kaso 2.2 a kan na bara. (Fa’iza Mustapha)