logo

HAUSA

Xi ya mika tuta ga rundunar samar da bayanai ta PLA

2024-04-19 20:51:58 CMG Hausa

A yau Juma’a, rundunar sojin kasar Sin wato rundunar ‘yantar da al’ummar kasar ta (PLA), ta kaddamar da wata rundunar samar da bayanai.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya mika tuta ga rundunar, yayin bikin kafa ta da ya gudana yau, a birnin Beijing.

Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar sojin kasar, ya nanata bukatar yin kokarin gaske wajen gina rundunar samar da bayanai mai karfi, wadda ta dace da zamani. (Fa’iza Mustapha)