logo

HAUSA

Wang Yi: Amurka ba ta da alfarma ko gatan kin biyayya ga dokokin kasa da kasa

2024-04-19 11:34:57 CMG Hausa

Jiya Alhamis, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da ’yan jaridu tare da takwararsa ta kasar Indonesia Retno Marsudi a birnin Jakarta, fadar mulkin kasar Indonesia.

A yayin taron, an ce a halin yanzu, gamayyar kasa da kasa na yin kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a yankin Gaza, yayin da ake kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya ba da gudummawarsa kan wannan aiki. Game da tambayar ko mene ne matsayin kasar Sin kan wannan batu?  Wang Yi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, rikicin yankin Gaza ya tsawaita zuwa rabin shekara, wanda ya haddasa mummunar barazanar jin kai da ba a taba ganin irin ta ba cikin karni na 21.

Ya ce kwamitin sulhun MDD ya amsa kiran gamayyar kasa da kasa, kuma yana ci gaba da binciken daftarin tsagaita bude wuta a yankin Gaza, amma, sau da yawa, kasar Amurka ita kanta kadai ta yi ta watsi da daftarori masu nasaba da hakan.

Kwanan baya, a karo na farko, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2728, inda aka yi kira da a tsagaita bude wuta a yankin Gaza, amma kasar Amurka ta ce daftarin ba shi da ikon hana ko wane bangare daukar mataki. Lamarin da ya bata ran kasashen duniya, ya kuma bayyana yadda kasar Amurka take son yi wa kasashen duniya mulkin kashin kai. Kaza lika hakan na nuna cewa, kasar Amurka tana bin manufar idan tana so, za ta bi dokokin kasa da kasa, amma idan ba ta so, shi ke nan, za ta yi kyamar dokokin.

Wang Yi ya kara da cewa, kasar Amurka, ba ta da alfarma ko gatan kin biyayya ga dokokin kasa da kasa. Don haka ake fatan Amurkan za ta daidaita tsohon ra’ayinta, tare da nuna goyon baya ga kuduri mai lamba 2728 a matsayin mambar MDD, domin yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen cimma burin tsagaita bude wuta a yankin Gaza.

(Mai Fassarawa: Maryam Yang)