logo

HAUSA

Dalibai miliyan 1.2 ne za su kasance cikin rukunin farko wajen cin gajiyar shirin bayar da rancen karatu a Najeriya

2024-04-19 13:58:26 CMG Hausa

Asusun da aka dorawa alhakin bayar da rance ga daliban manyan makarantun a Najeriya ya ce, yana sa ran dalibai miliyan daya da dubu dari biyu ne za su kasance cikin rukunin farko na wadanda za su fara cin gajiyar shirin wanda za a fara nan ba da dadewa ba.

Manajan daraktan asusun Mr. Akintunde Sawyerr ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 18 ga wata a birnin Legos yayin wani taro da ya gudanar da kungiyar marubuta al’amuran da suka shafi sha’anin ilimi ta kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Mr. Akintunde Sawyerr ya ce, duk dalibin da zai gabatar da bukatarsa ta neman bashin, wajibi ne sai ya nuna lambar rijistarsa ta jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa da lambar bankinsa ta sirri.

Ya ce, wadannan sharuddai guda biyu su ne muhimmai daga cikin abubuwan da gwamnati ke bukata kafin dalibi ya samu dacewa, kuma za a kasa bashin ne zuwa kaso biyu, na farko za a biya kudin makarantar dalibi kai tsaye zuwa ga asusun kwaleji, sai kuma kaso na biyu za a baiwa dalibi wani abu domin biyan bukatun kansa.

Manajan darkatan Asusun haka kuma ya ce, “Idan dalibi ya mika bukatar rance a zangon karatu na farko kuma ya dace, amma a zango na biyu kuma hukumar makarantar ce za ta kasance sheda ga dalibi domin ana iya samun dalibai da suke gaza iya ci gaba a zango na gaba.” (Garba Abdullahi Bagwai)