logo

HAUSA

Mutane fiye da miliyan 141 sun shiga ko fita daga kasar Sin a rubu’in farko na bana

2024-04-18 14:08:59 CMG Hausa

A yau Alhamis ne hukumar lura da shige da fice ta kasar Sin, ta sanar da manyan alkaluman lura da shige da fice na rubu’in farko na shekarar bana. 

Alkaluman sun nuna cewa, a rubu’in na farko, yawan mutane da suka shiga ko fita daga kasar bisa binciken hukumomin kasar sun zarce miliyan 141, adadin da ya karu da kashi 117.8 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.  (Safiyah Ma)