logo

HAUSA

Kasar Sin ta damu matuka game da yadda Amurka ke karfafa jibge sojoji a yankin Asiya da tekun Pasifik

2024-04-18 21:39:59 CMG Hausa

A yayin da yake mayar da martani game da karfafa jibge sojoji da Amurka ke yi a yankin Asiya da tekun Pasifik, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis, 18 ga wata cewa, kasarsa ta damu matuka game da abubuwan da batun ya shafa, kana ya bukaci Amurka ta mutunta damuwar wasu kasashe a fannin tsaro, kuma ta daina haifar da arangamar soji.

Rahotanni sun bayyana cewa, a kwanan baya rundunar sojojin kasa ta Amurka dake yankin Pacifik ta sanar da cewa, a wani bangare na atisayen hadin gwiwa da sojojin kasar Philippines, Amurka ta riga ta jibge na’urar harba makamai masu linzami mai cin matsakaicin zango ta “Typhon” a tsibirin Luzon na kasar Philippines. Wasu bayanai na cewa, matakin na Amurka na nufin kawo barazana ga kasar Sin.

Lin Jian ya kuma bukaci Philippines da ta fahimci ainihin burin matakin da Amurka ta dauka, da ma mummunan sakamakon da ke tattare da hadin gwiwa da Amurka. Kuma kada ta sadaukar da moriyarta ta fuskar tsaro don taimakawa Amurka yin wasu abubuwa masu hadari amma marasa riba, kuma kada ta ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba.

Har ila yau, Lin Jian ya mayar da martani kan kalaman da kasashen Amurka, Japan, da Philippines suka yi, game da batun tekun kudancin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, babu wani marufi da zai iya sauya ainihin ma’anar batun tekun kudancin kasar Sin, kana duk wani magudin siyasa da aka yi bisa hujjar kiyaye doka ba zai dakatar da kuduri da niyyar kasar ta Sin wajen kiyaye mulkin kai da cikakken yankin kasa da ma muradunta na teku ba, ko hakka babu, duk matakan za su bi ruwa. (Bilkisu Xin)