logo

HAUSA

AU ta yi kira ga kasashen Afirka da su inganta cin gajiyar yanar gizo

2024-04-18 14:06:49 CMG Hausa

 

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta yi kira ga kasashen Afirka da su inganta kwarewarsu ta cin gajiya daga yanar gizo, a gabar da nahiyar ke kara fuskantar barazana ta tsaron yanar gizo.

Kiran na kunshe ne cikin sanarwar da AUn ta fitar, ta cikin wata sanarwa da ta gabatarwa manema labarai a jiya Laraba, yayin taron karawa juna sani mai nasaba da diflomasiyyar yanar gizo, wanda ya hallara wakilai da dama daga ofisoshin diflomasiyyar kasashe mambobin kungiyar ta AU, ya kuma gudana tsakanin ranaikun 15 zuwa 16 ga watan nan na Afirilu a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Sanarwar ta hakaito kungiyar AUn na cewa, babban makasudin taron shi ne samar da wani mafari na ayyukan diflomasiyyar yanar gizo a matakin kungiyar, da fadakarwa game da barazanar tsaron yanar gizo da ake da ita, da muhimman sassa na mayar da hankali a fannin tsaron yanar gizo, da bude tattaunawa tsakanin bangarorin diflomasiyya, game da yanayi da fadin barazanar tsaron yanar gizo da ake ciki.   (Saminu Alhassan)