logo

HAUSA

Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-18 na dakon ’yan sama jannati

2024-04-17 14:18:51 CMG Hausa

Kasar Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-18 na dakon ’yan sama jannati. A jiya Talata aka dora kumbon a jikin rokar Long March-2F, a tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta Sin ta tabbatar.    (Saminu Alhassan)