Sharhi: Daidaiton da Sin da Jamus suka cimma zai taimakawa kawar da ra’ayi maras kyau daga yammacin duniya
2024-04-17 15:41:39 Sin Jamus
Jiya Talata rana ce ta karshe, a ziyarar wannan karo ta shugaban gwamnatin kasar Jamus a kasar Sin, inda a daidai wannan rana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shi a birnin Beijing na Sin. Yayin ganawarsu, shugabannin 2 sun yi musayar ra’ayi mai zurfi kan huldar dake tsakanin Sin da Jamus, da al’amuran kasa da kasa masu janyo hankulan al’ummun duniya.
Dukkan shugabannin 2 na Sin da Jamus sun bayyana kin amincewa da ra’ayin kariyar ciniki, da burinsu na karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2. A cewar bangaren Sin, ko a fannin harhada kayayyaki na gargajiya, irinsu injuna, da motoci, ko kuma ta fuskar sabbin masana’antu masu alaka da sauya akala zuwa fasahohin kare muhalli, da fasahar zamani ta dijital, da kirkirarriyar basira ko AI, da dai makamantansu, kasashen 2 na iya gudanar da hadin kai a tsakaninsu sosai, don neman cimma moriyar junansu. Wadannan maganganu sun tabbatar da alkiblar da za a nufa, a kokarin habaka hadin gwiwar kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki.
Hakika hadin gwiwar kasashen Sin da Jamus tana da amfani ga junansu, gami da daukacin kasashen duniya baki daya. Ta hanyar gudanar da hadin kai mai amfanar da juna, kasashen Sin da Jamus za su samar da karin gudunmawa ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. Haka zalika, hadin kansu, da daidaiton da suka cimma za su taimaka wajen kawar da ra’ayi maras kyau daga wasu kasashe na yammacin duniya, dake tare da burin lahanta zaman lafiya da damar ci gaba a duniya. (Bello Wang)