Yawan mutanen da suka zo kasar Sin daga ketare cikin farkon watanni uku na bana ya ninka sau uku
2024-04-29 16:34:34 CMG Hausa
Masu kallonmu, barka da war haka. Bayanin da hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin ta fidda ya nuna cewa, cikin farkon watanni uku na bana, yawan mutanen da suka zo kasar Sin daga ketare ya kai miliyan 13, adadin da ya ninka sau uku bisa na makamancin lokaci a bara. Wadannan mutanen da suka zo kasar Sin sun hada da masu yawon shakatawa, da kuma ‘yan kasuwa dake fatan habaka harkokinsu a kasuwannin kasar Sin.