logo

HAUSA

Firaministan Sin: Tarihin Canton Fair ya nuna yadda kasar Sin ke kokarin fadada bude kofarta ga kasashen waje

2024-04-17 21:05:44 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci shawarwari tare da wakilan baki ‘yan kasuwa na kasashen waje da suke halartar bikin baje-kolin hajojin da ake shigowa gami da fitar da su zuwa ketare na kasar Sin karo na 135, wanda aka fi sani da suna Canton Fair. Yayin taron wanda aka yi yau Laraba a birnin Guangzhou na lardin Guangdong, jami’in ya ce, tarihin Canton Fair, tarihi ne dake shaida yadda kamfanonin kasa da kasa ke more damammakin ci gaban kasar Sin, da cimma burin samun moriya tare, wanda kuma ke bayyana yadda kasar ke kokarin fadada bude kofarta ga kasashen waje, da shiga cikin kasuwannin duniya.

Li Qiang ya jaddada cewa, kasarsa za ta tsaya ga fadada bude kofa ga kasashen waje, da saukaka ayyukan kasuwanci da zuba jari, da ci gaba da samar da tabbaci ga harkokin cinikayya da tattalin arzikin dukkanin duniya bisa ci gabanta, tare kuma da samar da damammaki masu yawa ga kamfanonin kasa da kasa.

Wakilan baki ‘yan kasuwan ketare shida sun kuma gabatar da jawabai a yayin shawarwarin, inda suka bayyana yakini ga makomar tattalin arzikin kasar Sin, da bayyana fatan ci gaba da fadada kasuwanci a kasar Sin, da bayar da gudummawa ga gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci da tabbatar da samar da kayayyaki yadda ya kamata a duniya, ta hanyar halartar Canton Fair.

An kaddamar da bikin Canton Fair ne tun daga lokacin bazarar shekara ta 1957, wanda a kan yi shi sau biyu a kowace shekara a birnin Guangzhou, wato a lokacin bazara da na kaka. Canton Fair ya riga ya zama wani kasaitaccen bikin kasuwanci na kasa da kasa dake shafar fannoni daban-daban kuma mafi dogon tarihi a kasar Sin. (Murtala Zhang)