logo

HAUSA

Ministocin tsaro na kasashen Sin da Amurka sun yi tattaunawa ta kafar bidiyo

2024-04-17 14:32:58 CMG Hausa

Ministan tsaron kasar Sin janar Dong Jun, ya zanta ta kafar bidiyo tare da takwaransa na kasar Amurka Lloyd Austin a daren jiya, bisa agogon kasar Sin.

Jami’in na kasar Sin ya halarci tattaunawar ta biyo bayan gayyatar da bangaren Amurka ya yi masa, inda ya ce, la’akari da yadda shugabannin kasashen Sin da Amurka ke neman tabbatar da wani yanayi na karko, da kyautatuwar huldar dake tsakanin kasashen 2, kamata ya yi sojojin kasashen su zama ginshikin tabbatar da hakan.

Dong Jun ya kara da cewa, cikin batutuwa masu alaka da babbar moriyar tushe ta kasar Sin, batun yankin Taiwan yana da matukar muhimmanci. Kasar Sin za ta kula da batun yadda ya kamata, kuma ba za ta taba bari a lahanta babbar moriyarta ba.

Ya ce rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin ba za ta taba hakuri da yunkurin balle yankin Taiwan daga kasar Sin, da bangarorin ketare dake taimakon yunkurin ba. A halin yanzu, yanayin tsaro na yankin tekun kudancin kasar Sin yana da karko, saboda haka abu mafi dacewa shi ne, kasar Amurka ta fahimci kwararren matsayi na kasar Sin, da daukar hakikanan matakai na tabbatar da zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa, gami da wani yanayi mai karko na huldar dake tsakanin kasashen 2 da kuma sojojinsu.

Baya ga haka, bangarorin 2 sun kara yin musayar ra’ayi kan sauran batutuwan da ke jan hankulansu. (Bello Wang)