logo

HAUSA

Firaministan Sin ya zanta da shugaban gwamnatin Jamus

2024-04-17 10:22:47 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya zanta da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz jiya Talata a birnin Beijing. Yayin tattaunawar mista Li ya yi kira da a daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa sabon matsayi, mai kunshe da karin fahimtar juna, da cimma moriyar juna ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa.

Firaministan Sin ya ce a bana ake bikin cika shekaru 10 da kulla cikakkiyar huldar hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare, tsakanin Sin da Jamus. Kuma Sin a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Jamus, ta yadda za a bunkasa fahimtar juna ta hanyar shawarwari, da cimma moriyar juna ta hanyar hadin gwiwa.

Li ya kuma yi kira ga sassan biyu, da su taka rawar gani wajen ingiza shawarwari tsakanin gwamnatocinsu, da sauran tsare tsare a matakai daban daban, su samar da sabbin ginshikai na samar da ci gaban hadin gwiwa, kamar a fannin ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, da tattalin arziki na dijital, da kirkirarriyar basira ko AI, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Kaza lika sassan biyu su kara azama wajen goyon bayan musaya da hadin gwiwa tsakanin al’ummun su, da al’adu, da wasanni, da matasa, da ilimi, da binciken kimiyya da sauran sassa.

A nasa bangare, mista Scholz ya ce Sin muhimmiyar abokiyar hulda ce ta Jamus, kuma kasarsa a shirye take ta yi aiki da Sin wajen karfafa shawarwari, da tattaunawa a dukkanin matakai, da zurfafa hadin gwiwa a sassa daban daban irin su hada hadar kudade, da noma, da sauya akala zuwa ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da cin gajiyar sabbin makamashi, da ingiza musaya a fannonin al’adu, ilimi, wasanni da musaya tsakanin al’ummun su, kana da yin kokari tare wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi, da sauran kalubalen da duniya ke fuskanta, da ingiza ci gaban alakar kasashen biyu bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni.

Bayan tattaunawar manyan jami’an, Li da Scholz sun halarci taron kwamitin ba da shawarwari a fannin tattalin arziki na Sin da Jamus.   (Saminu Alhassan)