logo

HAUSA

GDPn kasar Sin a farkon watanni uku na bana ya kai fiye da dala triliyan 4

2024-04-16 10:42:34 CMG Hausa

 

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai a yau Talata, inda ya gayyaci mataimakin shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin Sheng Laiyun, don ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin Sin ya kasance a watan Janairu da Fabrairu da Maris na bana.

Bisa alkaluman da ya gabatar wa taron, yawan GDPn a wadannan lokuta ya wuce dala triliyan 4, wanda ya karu da kashi 5.3% bisa na makamancin lokacin bara, wanda kuma ya karu da kashi 1.6% bisa na watannin Oktoba da Nuwamba da Disamban bara. (Amina Xu)