logo

HAUSA

He Lifeng ya gana da tawagar jami’ai masu kula da harkokin tattalin arzikin Jamus

2024-04-16 21:48:32 CMG Hausa

Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, He Lifeng, ya gana da tawagar jami’ai masu kula da harkokin tattalin arzikin kasar Jamus, a yau Talata a babban dakin taron jama’a dake Beijing. Jami’an na ziyarar aiki a kasar Sin tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi hadin-gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu.

Jami’in ya ce, tattalin arzikin kasar Sin na bunkasa yadda ya kamata, kuma kasar za ta kara kokarin janyo jarin waje, da samar da wani kyakkyawan yanayin kasuwanci mai bin doka da oda ga kasa da kasa, da maraba da kamfanonin Jamus su fadada zuba jari a kasar ta Sin.

A nata bangaren kuma, shugabar tawagar jami’ai masu kula da harkokin tattalin arzikin Jamus, Franziska Brantner ta ce tana da yakinin sosai game da makomar tattalin arzikin kasar Sin, tana kuma mai fatan zurfafa hadin-gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, don cimma moriya tare. (Murtala Zhang)