logo

HAUSA

Rahoton da Birtaniya ta fitar dangane da “batun Hong Kong na rabin shekara” karya ce

2024-04-16 20:28:02 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian, ya bayyana a yau Talata cewa, wani rahoto da gwamnatin kasar Birtaniya ta fitar, mai taken wai “batun Hong Kong na rabin shekara” na cike da karairayi kuma ya jirkita gaskiya. Haka kuma shisshigi ne cikin harkokin yankin Hong Kong da harkokin gidan kasar Sin, da keta ka’idojin dokar kasa da kasa gami da muhimman manufofin dangantakar kasa da kasa, yana mai cewa, kasar Sin na nuna matukar takaici da rashin jin dadinta  game da batun.

Kakakin ya ce, tun bayan dawowar Hong Kong kasar Sin, gwamnatin kasar na yin tsayin daka wajen aiwatar da manufofin da suka shafi “kasa daya amma mai tsarin mulki biyu”, da “al’ummar Hong Kong su ne masu mulkar wurin”, kana Hong Kong na da ‘yanci sosai wajen gudanar da harkokinta da kanta. Kaza lika, tsarawa gami da aiwatar da dokar tabbatar da tsaron kasa, da ka’idojin tabbatar da tsaron kasa a yankin Hong Kong, na taimakawa sosai ga kiyaye tsaron kasa. (Murtala Zhang)