logo

HAUSA

Sin ta gabatar da rahoton binciken ikon mallakar fasaha na shekarar 2023

2024-04-16 09:33:55 CMG Hausa

 

Kwanan baya, hukumar mallakar fasaha ta kasar Sin ta gabatar da rahoton binciken ikon mallakar fasaha na shekarar 2023, alkaluma sun bayyana cewa, a halin yanzu, an daga karfin kare ikon mallakar fasaha a nan kasar Sin.

Kazalika, rahoton ya gabatar da bangarori hudu dake samun kyautatuwa a bangaren kare ikon.

Na farko, yawan fasahohin da ake amfani da su a cikin sana’o’i dabana-daban ya karu. A shekarar 2023, yawan fasahohin da aka yi amfani da su ya kai kashi 39.6% bisa dukkan fasahohin da aka kirkiro, adadin da ya karu da 2.9% bisa na 2022, hakan ya sa aka samun karuwa cikin shekaru 5 a jere.

Na biyu, hadin gwiwar sana’o’i da makarantu da kungiyoyin nazari, ya ba da muhimmanci wajen kirkiro muhimman fasahohi.

Na uku, halin kare ikon na rika samun kyautatuwa, a bara, karar da masu mallakar fasahohi suka kai kotu ya ragu da kashi 1% bisa na 2022.

Na karshe, yawan masu kirkirar fasahohi na samun karuwa matuka. (Amina Xu)