logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin zai ziyarci kasashen Indonesia da Cambodia da Papau New Guinea

2024-04-16 19:48:27 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai kai ziyarar aiki kasashen Indonesia da Cambodia da Papau New Guinea, daga ranar 18 zuwa 23 ga wata.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ne ya sanar da hakan a yau Talata. (Fa’iza Mustapha)