logo

HAUSA

Ganawar Xi Jinping da shugaban gwamnatin Jamus Scholz

2024-04-16 15:31:56 CMG Hausa

A safiyar ranar 16 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a Diaoyutai, wato gidan baki na kasa dake nan birnin Beijing.

Xi Jinping ya bayyana cewa, tsarin masana'antu da samar da kayayyaki na kasashen Sin da Jamus na da alaka da juna sosai, kuma kasuwannin kasashen biyu suna dogaro da juna matuka. Hadin gwiwar samun moriyar juna tsakanin Sin da Jamus ba abu ne mai hadari ba, illa dai tabbaci ne ga dorewar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma damar samar da kyakkyawar makoma. Ya kamata kasashen Sin da Jamus su gudanar da hadin gwiwarsu da kansu ba tare da wani ya shiga tsakani ba, da sa kaimi ga al'ummomin kasa da kasa da su kara tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, kamar sauyin yanayi, da rashin daidaituwar ci gaba, da rikice-rikicen shiyya-shiyya ta hanyar ayyuka masu inganci, da ba da gudummawa ga daidaito da kwanciyar hankali a duniya.

A nasa bangaren kuwa, Olaf Scholz ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Jamus da Sin na samun bunkasuwa mai kyau, kuma bangarorin biyu suna yin mu'amala ta kut-da-kut a dukkan matakai da kuma a fannoni daban daban. Bangaren Jamus na fatan karfafa tuntuba da yin aiki tare da kasar Sin don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta tare, kamar sauyin yanayi, kuma ta himmatu wajen kiyaye tsarin bangarori daban daban da zaman lafiya da ci gaban duniya. Kuma bai yarda da arangama ba.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake damunsu, kamar rikicin Ukraine da rikicin tsakanin Falesdinu da Isra'ila. (Yahya Mohammed)