logo

HAUSA

Bikin Canton Fair karo na 135 ya jawo hankalin ‘yan kasuwan Afrika fiye da dubu 30

2024-04-16 15:32:08 CMG Hausa

 

Yau Talata, a gun taron musayar dabarun habaka kasuwannin kasa da kasa na bikin baje kolin kayayyakin fice da shige na kasa da kasa na kasar Sin wato Canton Fair karo na 135, mataimakin daraktan bikin Zhou Shanqing ya bayyana cewa, a matsayin wani gaggarumin baje koli na kasa da kasa a bangaren ciniki, Canton Fair ya zama wata gada ga cinikayyar Sin da Afrika. ‘Yan kasuwan Afrika fiye da dubu 30 sun yi rajistar shiga wannan baje kolin, wanda ya karu matuka bisa na bukukuwan baje kolin da suka gabata.

An ce, kamfanoni daga kasashen Afrika 46 suna yin baje kolin kayayyakin da aka shigo da su Sin, ciki har da Masar da Uganda da Kenya da Zambiya da sauransu, inda kayayyakin da za a gabatar sun hada da laturoni na gida da kayayyakin karfe da na gina gidaje, da kayayyakin masarufi da abinci da sauransu. (Amina Xu)