logo

HAUSA

Xi ya gabatar da ka’idoji hudu don warware rikicin Ukraine

2024-04-16 15:57:03 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya gabatar da shawarwari guda hudu don hana rikicin kasar Ukraine kara tabarbarewa, da mai do da zaman lafiya tun da wuri.

Xi ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz dake ziyara a nan Beijing, kuma shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi mai zurfi kan rikicin Ukraine a tattaunawarsu.

Xi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki a yanzu, domin hana rikicin kara tabarbarewa, ya kamata dukkan bangarorin su hada kai don dawo da zaman lafiya cikin sauri. Bisa wannan dalilin ne ya gabatar da shawarar ka’idoji guda hudu.

“Na farko ya kamata mu ba da fifiko wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da nisantar son rai. Na biyu kuma mu kwantar da al’amura, kada mu kara ruruwa wutar fitina. Na uku kuma mu samar da yanayin da za a maido da zaman lafiya, sannan mu guji kara tayar da hankula. Na hudu, ya kamata mu rage mummunan tasirin rikici kan tattalin arzikin duniya, tare da gujewa kawo tsaiko ga daidaton tsarin masana'antu da samar da kayayyaki a duniya." (Yahaya Mohammed)