logo

HAUSA

Mataimakin firaministan Sin ya gana da shugabar hukumar USPTO a birnin Beijing

2024-04-15 21:16:48 CMG Hausa

A yau Litinin ne mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya gana da shugabar hukumar lura da rajistar ikon mallakar fasahohi ta Amurka ko USPTO Kathi Vidal a birnin Beijing

Yayin ganawar ta su Ding Xuexiang, ya ce Sin na dora muhimmancin gaske ga batun kare ikon mallakar fasaha, kuma a shirye take ta fadada hadin gwiwa na zahiri tare Amurka a fannin, da shawo kan damuwar sassan biyu, da yaukaka adalci, da samar da yanayi na gaskiya maras nuna wariya na gudanar da kasuwanci, tare kuma da bayar da babbar gudummawa ga bunkasar akalar ta da Amurka.

A nata bangare kuwa, Vidal cewa ta yi USPTO na dora matukar muhimmanci ga hadin gwiwar ta da Sin a fannin kare ikon mallakar fasahohi, kuma a shirye take ta karfafa tattaunawa, da musaya, da hadin gwiwa, ta yadda za a kai ga samar da hadimomi masu nagarta ga sassan kirkire kirkire, tare da cimma nasarar samar da sauye sauye, da aiwatar da nasarorin da ake samu daga kirkire kirkire. (Saminu Alhassan)